in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in kasar Sin ya halarci taron manyan wakilan BRICS a harkokin tsaro karo na 6
2016-09-16 12:21:32 cri

A jiya Alhamis ne wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi, ya halarci taron manyan wakilan kasashe mambobin kungiyar BRICS, game da harkokin tsaro karo na 6. Taron dai ya zamo na share fagen bude taron shugabannin kungiyar BRICS karo na 8 ne da za a yi a watan Oktobar bana a birnin Goa na kasar Indiya.

A yayin taron, an yi musayar ra'ayoyi dangane da batutuwan tsaro a yanar gizo, da tabbatar da isasshen makamashi, da yaki da 'yan ta'adda, da nazarin halin da ake ciki a yammacin Asiya, da arewacin Afirka da Gabas ta Tsakiya, an kuma cimma daidaito game da inganta hadin kan kasashen BRICS.

Yang Jiechi ya ce, ci gaba da hadin kan kasashen BRICS, da zurfafa hadin gwiwarsu, zai bude sabon shafi na bunkasar kasashen BRICS. Ya ce kasar Sin za ta zama shugaba mai kula da hadin kan kasashen BRICS a shekara mai zuwa, za kuma ta share fagen gudanar da taron shugabanni, da taron manyan wakilai masu kula da harkokin tsaro, da taron ministocin harkokin waje, da sauran tarurruka cikin himma da kwazo, a kokarin hada kai da sauran kasashen BRICS wajen kara azama kan ci gaba da inganta hadin gwiwar a-zo-a-gani a tsakanin kasashen na BRICS. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China