in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da gwamnan sabon bankin neman ci gaba na BRICS
2016-02-28 12:54:27 cri
A jiya Asabar, 27 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da gwamnan sabon bankin neman ci gaba na kungiyar BRICS Kundapur Vaman Kamath, gabanin kulla yarjejeniyar kafa hedkwatar bankin a birnin Shanghai na kasar Sin.

A yayin ganawar tasu, Wang Yi ya bayyana cewa, kafa wannan reshe ya kasance da wani muhimmin shirin da zai karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar BRICS, kuma bangaren Sin na fatan bankin zai iya tallafawa membobin kungiyar da ma sauran kasashe masu tasowa, wajen gudanar da wasu muhimman ayyuka, ta yadda za a iya ingiza mu'amala da tuntubar juna tsakanin kasa da kasa, da bunkasa ayyukan samar da sabbin makamashi a duniya.

Sannan Wang Yi ya yi fatan bankin zai kasance bankin dake iya samar da hidima bisa kwarewa, kuma ba tare da boye kome ba wajen ba da tallafi ga ayyuka na kare muhalli a karnin 21 da muke ciki, domin kokarin kyautatawa, da yin gyare-gyare ga tattalin arzikin kasashen duniya gaba daya.

A nasa bangaren, Mr. Kamath cewa ya yi sabon bankin neman ci gaba na BRICS na nuna matukar godiya ga goyon bayan da gwamnatin kasar Sin, da hukumomin birnin Shanghai suka nuna masa, a lokacin da ake kokarin kafa shi. Ya ce bankin neman sabon ci gaba na BRICS, zai yi kokarin cimma burin da gwamnatocin kasashe 5 na BRICS da jama'arsu suke da shi, tare da kokarin bude kofarsa ba tare da bata lokaci ba, ta yadda zai iya taka rawar gani wajen ci gaban kasashen BRICS, da ma sauran kasashe masu tasowa, ya kuma inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China