in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana da babban fata game da sabon bankin ci gaban BRICS reshen Afrika
2016-03-03 10:28:38 cri

A cikin shirin da ake yi na bude reshen bankin ci gaba na kungiyar kasashen BRICS a wannan watan a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta kudu, ana da babban fatan a kan bankin daga dukkan bangarori na kasar.

Bankin dai kasashen Brazil, Rasha, India, Sin da Afrika ta kudu wanda suka hada sunan BRICS suka kaddamar da shi.

Ana sa ran bankin zai samar da kudade a bangaren karancin kayayyakin more rayuwa, zai kuma taimaka a sha'anin tattalin arzikin duniya, in ji Cyril Prinsloo na cibiyar yin nazari kan harkokin kasa da kasa ta Afrika ta kudu, a bayanin da ya yi a wani taron kara wa juna sani dangane da bankin ci gaban.

Mr Prinsloo ya ce, cibiyar Bretton Wood, bankin duniya da kuma asusun ba da lamuni na duniya wadanda duk aka kafa su bayan yakin duniya na biyu ba su bayyana ainihin abin da ake fusknata a yau.

Kasashen BRICS da ci gaban tattalin arziki sun sha fama da takaici da cibiyar Bretton Wood ke ba su, don haka suke fatan bankin ci gaban zai zama daban a ayyukan shi.

Ya kara da cewar, bankin ci gaban har ila yau ana fatan zai samar da rance a kudin mazauna kasar maimakon yadda asusun ba da lamuni da bankin duniya wadanda dalar Amurka kadai suke bayarwa.

Ita ma a nata tsokacin, Marianne Buenaventure Goldman, mai ba da shawara a majalisar zartarwar Oxfam, wata kungiyar ba da agaji da tallafin ci gaba, ta ce, suna fatan bankin ci gaban na BRICS zai lura da wassu ayyukan MDD a shirinta na dauwamammen ci gaban muradun karni SDGs.

Mai shari'a Nomonde Nyembe na jami'ar Witwatersrand na kasar Afrika ta kudu, cewa ya yi suna fatan bankin ci gaban zai yi aiki daban da sauran masu samar da kudade na gargajiya.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China