in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya da sabon bankin raya kasashen kungiyar BRICS sun daddale takardar fahimtar juna
2016-09-10 12:55:08 cri

Bankin duniya da sabon bankin raya kasashen kungiyar BRICS sun daddale takardar fahimtar juna a jiya ranar 9 ga wata a birnin Washington dake kasar Amurka don kara hadin gwiwarsu a fannin ayyukan more rayuwa.

Bisa takardar da suka daddale, bangarorin biyu za su nemi damar tattara kudi, da sa kaimi ga yin mu'amala kan ilmi da fasahohi da kuma yin mu'amala a tsakanin ma'aikatan bangarorin biyu. Hukumomin biyu sun bayyana cewa, za su yi hadin gwiwa da dora muhimmanci sosai a fannin ayyukan more rayuwa.

A wannan rana, shugaban bankin duniya Kim Yong ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, daddale takardar fahimtar juna zai sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu. Ya ce, idan hukumomin kasa da kasa sun yi hadin gwiwa da nuna goyon baya ga kasashe mafi talauci kana su samu ci gaba ba tare da yin la'akari da bambance-bambance ba, to hakan zai kara kawo moriya ga mutane masu fama da talauci.

Shugaban sabon bankin raya kasashen kungiyar BRICS Vaman Kamath ya bayyana a cikin sanarwa cewa, ya nuna godiya ga bankin duniya da ya nuna goyon baya ga bankinsa yayin da aka kafa shi, kana yana fatan za a kara yin hadin gwiwa a tsakanin bankunan biyu.

An kafa sabon bankin raya kasashen kungiyar BRICS a shekarar 2014, wanda ita ce hukumar kasa da kasa da kasashen Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afirka ta Kudu suka kafa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China