A yammacin wannan rana, wakilan kasashen BRICS sun yi jawabi, inda suka bayyana cewa, batun samun bunkasuwa ya kasance tushen kawar da talauci, kuma talauci shi ne jigon barkewar rikice-rikice da dama a dukkanin fadin duniya. Kaza lika samun bunkasuwa na da tasiri ga kare hakkin dan Adam, yayin da kawar da talauci ya zama babban sharadi da burin samun dauwamammen ci gaba, da raya zamantakewar al'umma da kiyaye adalci, tare kuma da gina muhallin halittu.
Kasashen BRICS sun bayyana cewa, ya kamata a girmama manufofin kasashen duniya game da samun bunkasuwa, da kauracewa amfani da manufa guda, kasancewar kasashe da dama ne da mabambantan matakan bunkasuwa, da tarihi, da yanayin da kasashensu ke ciki, lamarin da ya sa ya kamata a sa kaimi ga kasashen duniya, wajen inganta dabarun raya kasashensu, da shirin samun dauwamammen ci gaba na shekarar 2030 na bai daya tare.(Bako)