Kasashen BRICS na wakiltar muhimman tattalin arzikin kasashe masu tasowa guda biyar na duniya wato Brazil, Rasha, Indiya, Sin da Afrika ta Kudu.
Dangantakarsu a bangaren watsa labarai na iya taimakawa wajen kafa wani sabon tsarin duniya na sadarwa bisa adalci, in ji mista He.
Ya gaya ma Xenia Fedorova, daraktar kamfanin dillancin labarai na Ruptly, cewa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a shiye yake wajen karfafa dangantakarsa tare da kafofin watsa labarai na kasar Rasha, domin bunkasa fahimtar juna da abokantaka.
Ruptly, wani reshen Russia Today (RT), ya kasance wata hukumar dillancin watsa labaran kasa da kasa dake da hedkwata a birnin Berlin na kasar Jamus. Yana harhada rahotannin bidiyo kai tsaye bisa lokaci da kuma hotunan tarihi ga dukkan kafofin watsa labarai. (Maman Ada)