in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EU ta kalubalanci Birtaniya da ta hanzarta shirin ficewa daga EU
2016-09-16 12:19:54 cri

Shugaban hukumar kungiyar Tarayyar Turai wato EU Jean-Claude Juncker, ya kalubalanci kasar Birtaniya da ta hanzarta shirin ficewarta daga EU.

Junker ya bayyana hakan ne a yayin cikakken taron majalisar Turai da aka gudanar a birnin Strassburg na kasar Faransa, inda ya gabatar da jawabin shekara-shekara kan yanayin da kungiyar EU take ciki,

Mista Juncker ya jaddada cewa, idan Birtaniya ta shirya ci gaba da kasancewa cikin kasuwar bai daya ta Turai bayan da ta fice daga EU, to, ya zama tilas ta martaba ka'idar mu'amalar ma'aikata ba tare da gindaya wani sharadi ba. Haka kuma ba za ta tsara abun da take so, ko ta ki amincewa da abun da ba ta so ba. Jami'in ya ce, akwai bukatar EU ta inganta hadin kai wajen tinkarar kalubalen da ake fuskanta a halin yanzu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China