Tsohon firaministan kasar Birtaniya Cameron ya sanar da yin murabus daga majalisar dokokin kasar
Tsohon firaministan kasar Birtaniya David Cameron ya bayyana a jiya Litinin cewa, zai yi murabus daga memban jam'iyyar Conservative a majalisar dokokin kasar, domin ba ya son ra'ayinsa a majalisar ya yi tasiri ga sabuwar firaministar kasar Theresa May.
Cameron ya bayyanawa 'yan jarida na gidan rediyon BBC cewa, ya dade yana tunanin yanke wannan kuduri, domin a matsayin na tsohon firaminista, ba dace ya zama dan bayan fage a majalisar dokokin kasar ba. (Zainab)