A cikin sakon, Li Keqiang ya bayyana cewa, a wadannan shekaru ana ta samun ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Birtaniya, kana shugabannin kasashen biyu sun kai ziyara ga juna, da raya hadin gwiwar da ke tsakaninsu da kuma yin mu'amalar al'adu yadda ya kamata. Sin ta nuna yabo ga gwamnatin kasar Birtaniya bisa ga kokarinta na inganta hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin, kuma Sin tana son hada kai tare da kasar Birtaniya wajen zurfafa dangantakar dake tsakaninsu ta yadda za ta amfanawa jama'arsu. (Zainab)