Haka kuma, bisa labarin da jaridar Sunday Times ta kasar Birtaniya ta samar, an ce, hukumar dake kula da harkokin ficewar kasar daga kungiyar EU da harkokin diflomasiyya ba ta sami isassun ma'aikata ba, shi ya sa, mai iyuwa, kasar Burtaniya za ta jinkirta lokacin fara gudanar da ayyukan ficewarta daga kungiyar EU zuwa karshen shekarar 2017.
Dangane da wannan harka, kakakin fadar firaministan kasar Birtaniya ya ce, aikin ficewar kasar daga kungiyar EU wani muhimmin aiki ne mai nauyi kuma na dogon lokaci, shi ya sa, ba za a fara wannan aiki ba a hukunce kafin karshen shekarar bana, amma kakakin bai bayyana ko yaushe za a fara gudanar da ayyukan da abin ya shafa ba.
Bisa dokokin kungiyar EU da abin ya shafa, ya kamata mambar dake son fice daga kungiyar ta bi kuduri mai lamba 50 na yarjejeniyar Lisbon, sa'an nan ta fara ayyukan ficetarta daga kungiyar EU, amma wannan aiki na dogon lokaci ne, a kalla za a kashe shekaru biyu wajen kammala ayyukan da abin ya shafa. (Maryam)