in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Theresa May ta yi rantsuwar kama aikin sabuwar firaministar Birtaniya
2016-07-14 12:50:16 cri
A jiya Laraba 13 ga wata, firaminsitan kasar Birtaniya David Cameron‎ ya mika takardar murabus ga sarauniyar Birtaniya Elizabeth II, daga baya a wannan rana Theresa May ta zama sabuwar firaminsitar kasar tare da nada sabbin ministocin gwamnatin kasar.

Theresa May da mijinta Philip John May sun isa fadar firaministan kasar tare da yin jawabi. A cikin jawabinta, May ta yi alkawarin kawar da rashin adalci a zamantakewar al'ummar kasar, da kuma tinkarar kalubale bayan da kasar ta janye daga kungiyar EU.

Bayan da Theresa May ta shiga fadar firaministan kasar, ta nada sabbin ministocin gwamnatin kasar nan da nan. An nada tsohon ministan harkokin wajen kasar Philip Hammond a matsayin ministan kudi, tsohon magajin birnin London kuma babban jagora kan janyewar Birtaniya daga EU Boris Johnson ya zama ministan harkokin wajen kasar, tsohon ministan kula da makamashi da sauyin yanayi na kasar Amber Rudd a matsayin ministan harkokin cikin gida, kuma ministan tsaron kasar Michael Fallon ya ci gaba da zama mukaminsa.

Hakazalika kuma, Theresa May ta nada Davies David a matsayin ministan kula da harkokin kasar na janyewa daga EU, wannan mukami sabo ne da aka kafa a wannan karo. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China