Kafofin yada labarai sun yi amfani da maganar kakakin madam Theresa Mary May cewa, sabuwar gwamnatin kasar na fatan yin nazari kan aikin Hinkley Point cikin taka-tsantsan. Birtaniya na dora muhimmanci kan dangantaka tsakaninta da Sin. Ta ce, Sin na taka muhimmiyar rawa a harkokin duniya, da tattalin arzikin duniya, da kuma jerin batutuwan duniya, shi ya sa kasar za ta kokarta kafa dangantaka mai karfi tsakaninsu.
A sa'i daya, kakaki ba ta yi tsokaci ba cewa, ko ana sake yin la'akari da aikin Hinkley Point sabo da tsaron kasa. Ta furta cewa, kasar Birtaniya tana ci gaba da bude kofa ga kamfanoni, da zummar samun jari da za a zuba a kasar daga ketare. (Fatima)