Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Birtaniya ta gabatar da sabon jerin sunayen kungiyoyin ta'addanci da kasar take yaki da su a ranar 15 ga wannan wata, inda kusan kungiyoyi 70 da gwamnatin kasar ta hana su bisa dokokin yaki da ta'addanci su gudanar da aikinsu a shekarar 2000, ciki har da kungiyar Turkistan Islamic.
An yi bayani game da hakikanin yanayin kungiyar Turkistan Islamic, inda aka yi nuni da cewa, kungiyar kungiya ce ta ta'addanci da kawo baraka, wadda aka kafa a yammacin kasar Sin a shekarar 1989, kuma yunkurinta shi ne kawo baraka a yankin arewa maso yammacin kasar Sin. (Zainab)