Tashar yanar gizo ta dandalin kasar Sudan ta labarta a ranar 14 ga wata cewa, gwamnatin Sudan ta soki majalisar dokokin kasar Amurka a kwanan baya, saboda ta zartas da wata doka, inda ta yarda da wadanda harin "9•11" ya rutsa da iyalansu da su kai gwamnatin Saudiyya kara. A ganin gwamnatin Sudan, shirin dokar ta saba wa ka'idojin MDD.
Bayan abkuwar harin ta'addanci na "9•11", wasu iyalan wadanda harin ya shafa suna ganin cewa, kungiyar ta'addanci ta al-Qaeda ta samu taimakon kudi ne daga Saudiya, don haka gwamnatin Saudiyya tana da hannu a harin. Ban da haka kuma, an ce, wasu mutane 15 daga cikin masu yin fashin jiragen sama su 19, dukkansu 'yan Saudiya ne. Saboda haka wadanda suka tsira a harin "9•11" da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu cikin harin su kai gwamnatin Saudiyya kara a kotun Amurka tare da neman a biya su diyya.
A ranar 9 ga wata, majalisar wakilan Amurka ta zartas da shirin dokar, inda ta shirya yarda da wadanda harin "9•11" ya shafa da kuma iyalansu da su kai gwamnatocin kasashen waje kara a kotun Amurka, wadanda ake tuhumarsu da laifin goyon bayan 'yan ta'adda. An zartas da shirin dokar a watan Mayun bana a majalisar dattawan Amurka, wadda daga baya shugaba Barack Obama zai sa hannu a kanta. (Tasallah Yuan)