in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan da UNHCR za su taimakawa 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu
2016-09-02 09:28:15 cri
Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Sudan da babbar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD sun sanya hannun kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da nufin taimakawa 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu da ke zaune a jihohin gabashin Darfur, da kudanci da yammacin Kordofan,White Nile da kuma Khartoum.

Kwamishinan kula da harkokin 'yan gudun hijira na Sudan Hamad al-Jazouli da wakiliyar ofishin kula da 'yan gudun hijira na MDD da ke Sudan Angela Li Rosi ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin bangarorin biyu..

Al-Jazouli ya bayyana a lokacin bikin sanya hannun cewa, hukumar UNHCR ce za ta tsara yadda za a fara yiwa 'yan gudun hijirar rijista da kuma kafa sansanonin da za a tsugunar da su.

Rahotanni na nuna cewa, bayan barkewar tashin hankalin baya-bayan nan a Juba,babban birnin kasar Sudan ta kudu, an yi rijistar 'yan gudun hijira kimanin 500,000. Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta kasar Sudan ta yanke shawarar cewa, za ta rika daukar 'yan Sudan ta kudu da suka bar kasarsu a matsayin 'yan gudun hijira.

Bayanan da MDD ta fitar a tsakiyar watan Agusta sun nuna cewa, kimanin 'yan gudun hijira 90,000 ne suka shiga kasar Sudan daga Sudan ta kudu tun farkon shekarar nan ta 2016. Alkaluman baya-bayan nan suna nuna cewa, kusan 'yan kasar Sudan ta kudu 198,600 ne suka shiga kasar Sudan, tun bayan barkewar rikici a kasar a tsakiyar watan Disamban shekarar 2013.

Galibin 'yan gudun hijirar Sudan ta kudu dai suna zaune ne a sansanoni 7 da ke jihohin White Nile da gabashi da yammacin Darfur da kuma birnin Khartoum na kasar ta Sudan.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China