Mataimakin shugaban kasa na daya na Sudan ta kudu Taban Deng wanda ya shaidawa taron manema labarai hakan a jiya Talata bayan ganawarsa da takwaransa na kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya ce, daga yanzu ba za a sake tayar da rikici a Sudan ta kudu ko kuma wani wuri a nahiyar Afirka ba.
Deng ya ce, za su yi wa kansu kiyamul laili, don ganin sun inganta rayuwar jama'arsu ta hanyar samar musu da kayayyakin more rayuwa har ma da abinci.
Ya ce, gwamnatinsa a shirye ta ke wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma ta yadda ba za a sake komawa gidan jiya ba.
A jiya Talata ne dai Deng ya isa birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu don tattaunawa da Ramaphosa game da shirin wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu.(Ibrahim)