in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sudan ta Kudu ta amince da kudurin MDD na kara tura mata sojojin wanzar da zaman lafiya 4000
2016-09-06 11:03:49 cri
A daren ranar Lahadi 4 ga watan nan ne gwamnatin rikon kwarya ta hada kan al'ummomin Sudan ta Kudu, ta bayyana cewa ta amince da kudurin da kwamitin sulhun MDD ya zartas, na kara yawan sojojin wanzar da zaman lafiya 4000 zuwa kasar.

Ministan harkokin majalissar ministocin kasar Sudan ta Kudun, Martin Elia Lomoro, shi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa domin kyautata yanayin tsaro a kasar, gwamnati ta riga ta amince da kudurin kwamitin sulhun MDD na jibge sojojin wanzar da zaman lafiya.

A ranar 2 ga wata, tawagar kwamitin sulhun MDD ta isa birnin Juba, helkwatar kasar Sudan ta Kudun, domin nazartar yanayin tsaro da ake ciki a kasar. Rahotanni na cewa bayan ganawar shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit da tawagar kwamitin sulhun MDD a ranar 4 ga wata, gwamnatin kasar ta amince da wannan kuduri.

Mr. Lomoro ya kara da cewa, gwamnatin Sudan ta Kudu za ta tattauna da wakilan kwamitin sulhun game da yadda za a jibge wadannan sojojin wanzar da zaman lafiya 4000. A sa'i daya, gwamnatin kasar za ta tsara wani shiri tare da tawagar MDD a Sudan ta Kudun, za kuma a dauki kwararan matakai, na kara kawar da shingen da tawagar MDD za ta iya fuskanta wajen gudanar da aikinta a Sudan ta Kudun. (Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China