in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sudan ta kama bakin haure 190 a kan iyakarta da Libya
2016-08-31 09:51:58 cri

Mahukuntan kasar Sudan sun sanar da kama mutane 190 wadanda suka hada da mata da kananan yara daga kasashe daban-daban wadanda ke kokarin shiga cikin kasar ta kan iyakar Libya ba bisa ka'ida ba.

Darektan kula da harkokin shigi da fice da rajistar 'yan kasa laftana janar na 'yan sanda Awad al-Neel Dahiya, ya ce, sojojin kasar sun yi nasarar dakatar da motoci guda dauke da bakin haure 190 a kan iyakokin Sudan da Libya.

Jami'in ya kuma tabbatar da cewa, yanzu haka an mika su ga hannun 'yan sanda a birnin Khartoum domin su gudanar da bincike kamar yadda doka ta tanada. Yana mai cewa, Sudan za ta ci gaba da hada kai da hukumomin da suka dace don kare kan iyakokinta daga bakin haure, da tarwatsa gungun masu fataucin jama'a da sauran miyagun ayyuka.

Laftana Awad ya ce, 'yan gudun hijira suna amfani da Sudan a matsayin wani zango a kan hanyarsu ta zuwa kasashen Turai, inda ya kara jaddada kudurin kasarsa na aiwatar da yarjejeniyar kasa da kasa da aka cimma game da magance kaurar jama'a ba bisa ka'ida ba.

A nasa jawabin babban hafsan sojojin kasa na Sudan, Staff laftana janar Assir Husein Bashir ya zargi wasu kasashen Turai da hannu a ayyukan fataucin jama'a. Yana mai cewa, kungiyar 'yan tawayen yankin Darfur sun rikide zuwa masu fataucin jama'a, tun bayan da suka yi karfi a yankin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China