Wani jami'in kungiyar Red Crescent ta kasar Sudan, ya bayyana a jiya Talata cewa, ruwan sama kamar da bakin kwarya ya sauka a wurare da dama a kasar, wanda hakan ya sabbaba aukuwar ambaliyar ruwa da ta hallaka mutane a kalla 80, yayin da wasu mutanen fiye da dubu 160 suka shiga mawuyacin hali.
An ba da labari cewa, kungiyar Red Crescent ta Sudan ta samu tallafi daga kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da kungiyar Red Cross ta kasar Sin. A halin yanzu kuma, kungiyoyin masu aikin ceto na kasar Sudan sun fara ba da rumfuna, da abubuwan samar da haske, da abinci, da magunguna da kuma sauran kayayyakin masarufi ga al'ummun da wannan bala'i ya shafa. (Lami)