Tawagar na karkashin jagorancin wakilan dindindin na kasar Senegal da na Amurka dake MDD. Kuma zata gana da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da sauran manyan jami'an gwamnatin wucin gadi, a cewar tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Sudan ta Kudu (MINUSS) a cikin wata sanarwa.
Wannan ziyara ta zo daidai bayan sabbunta wa'adin MINUSS. A ranar 12 ga watan Augusta, kwamitin sulhu ya sake sabbinta wa'adin MINUSS har zuwa ranar 15 ga watan Satumban shekarar 2016 tare kuma da bada umurnin kafa wannan rundunar bada kariya ga shiyyar mai kunshe da sojoji dubu hudu, a cikin tawagar MINUSS, dake da nauyin tabbatar da wani yanayi na tsaro da shige da fice ba tare da matsala a Juba da kewaye.
Haka kuma rangadin nada manufar ingiza shawarwarin zaman lafiya ta yadda MINUSS zata cigaba da aiki tare da gwamnati domin kyautata matsalar tsaro da jin kai a Sudan ta Kudu, musammun ma rundunar bada kariya ta shiyya, wani sabon ginshiki na sabon wa'adin tawagar MINUSS.
A tsawon rangadinsu na kwanaki uku, mambobin tawagar kwamitin sulhu zasu kai ziyara a sansanin MINUSS dake Wau, da kuma ganawa da 'yan gudun hijira dake wurin, in ji sanarwar.
Mambobin tawagar zasu kuma gana da kungiyoyin fararen hula, shugabannin jama'a, da kuma kungiyoyin mata da matasa.
Bayan rangadinsu na kwanaki uku a Sudan ta Kudu, tawagar zata isa Addis Abeba na kasar Habasha a ranar Litinin, domin tattaunawa tare da wakilan kungiyar IGAD da kuma mambobin kwamitin zaman lafiya da tsaron na kungiyar AU. (Maman Ada)