Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Amurka, Peter Cook ya bayyana a cikin wata sanarwar cewa, Abu Muhammad Al-Adnani ya mutu ne a sakamakon harin da jirgin saman sojojin Amurka suka kai a ranar 30 ga watan Agusta a Syria. Sojojin Amurka za su ci gaba da kaddamar da hare-haren da suke kaiwa har sai sun ga bayan manyan jagororin kungiyar IS.(Fatima)




