in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan tsaron Amurka ya sanar da kara yawan sojoji 560 a kasar Iraki
2016-07-12 10:49:44 cri

Ministan tsaro na kasar Amurka Ashton Carter ya kai ziyarar ba zato a kasar Iraki a jiya Litinin, kana ya yi shawarwari tare da firaministan Iraki Haider Al-Abad da kuma sauran jami'an kasar. Ashton Carter ya sanar a wannan rana cewa, kasar Amurka za ta kara tura sojoji 560 zuwa kasar, domin ba da taimako ga sojojin kasar Iraki wajen kwace muhimmin birnin Mosul.

A ranar 9 ga wannan wata, sojojin kasar Iraki sun karbe sansanin sojojin sama na Qayyarah dake da nisan kilomita 64 daga kudancin birnin Mosul. Mr. Carter ya bayyana a jiya Litinin cewa, hakan ya shaida cewa, sojojin Iraki suna da niyya sosai wajen yaki da kungiyar IS. Kasar Amurka za ta samar da karin taimako ga kasar Iraki tare da kawancen kasa da kasa.

Ma'aikatar tsaro ta kasar Amurka ta ba da sanarwa a jiya Litinin cewa, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya tsai da kuduri bayan da ya tattauna tare da Ashton Carter da shugaban taron hafsan-hafsoshin kasar Amurka Joseph Dunford cewa, kasar Amurka za ta kara tura sojoji 560 zuwa kasar Iraki domin yaki da kungiyar IS.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China