in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IS ta dauki alhakin harin da aka kai a birnin Nice na kasar Faransa
2016-07-17 12:13:32 cri
Kafofoin watsa labaru na kasar Faransa a ranar Asabar sun watsa wani labarin da kamfanin dillancin labaru na Amaq mallakar kungiyar masu kaifin ra'ayi Islama IS ya gabatar cewa, kungiyar IS ta dauki alhakin harin ta'addancin da aka kai a birnin Nice na kasar Faransa, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 84.

Cikin wannan labarin da kamfanin Amaq ya gabatar, an ce wani sojan kungiyar IS ne ya kaddamar da harin kan jama'a mazauna birnin Nice.

A daren ranar Alhamis bisa agogon wurin, wani dan asalin kasar Tunisia mai shekaru 31 a duniya ya tuka wata babbar mota wadda ta kutsa kai cikin taron jama'a dake kallon wasan wuta da aka shirya don murnar bikin ranar kafuwar kasar Faransa a birnin Nice, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 84, gami da raunatar wasu 202. Cikinsu mutane 52 sun samu munanan raunuka. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China