Ma'aikatar tsaron ta bayyana cewa, mako guda kafin hakan, kasar Faransa ta kai farmaki sau da dama ta sama, kan na'urorin kungiyar ta IS dake dab da birnin Mosul na kasar Iraki.
A ranar 13 ga watan Nuwambar shekarar bara ne dai aka kaddamar da farmakin ta'addanci a birnin Paris, fadar mulkin kasar Faransa, hare haren da suka haddasa rasuwar mutane a kalla 130, yayin da mutane kimanin 350 suka ji rauni.
Kungiyar IS dai ta sanar da daukar alhakin kai farmakin, matakin da ya sanya sojojin kasar Faransa karfafa matakan soja da take dauka a kan kungiyar ta IS dake kasashen Iraki da Syria. (Bilkisu)