in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar tsaron Amurka ta tabbatar da kaiwa kakakin IS hari
2016-08-31 15:29:05 cri
Jiya Talata 30 ga wata, hukumar tsaron Amurka ta gaskata cewa, kungiyar hadin gwiwar kasa da kasa dake yaki da IS karkashin jagorancin kasar Amurka ta kaiwa kakakin kungiyar IS Abu Mohammed al-Adnani hari a wannan rana.

Cikin wata sanarwar da kakakin hukumar tsaron kasar Amurka Peter Cook ya fitar, an ce, an kaiwa al-Adnani harin ne a Lardin Aleppo na kasar Syria, a halin yanzu kuma, sojojin Amurka suna gudanar da bincike kan sakamakon wannan matakin sojan da aka dauka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China