in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron koli na NATO ya sanar da kara karfin yaki da kungiyar IS
2016-07-10 13:27:11 cri

Babban sakataren kungiyar NATO Jens Stoltenberg ya bayyana a Warsaw, hedkwatar mulkin kasar Poland cewar, NATO za ta kara samar da goyon baya ga kawancen kasashe masu yaki da kungiyar IS mai tsattauran ra'ayi, da kuma kara yawan harkokin da za ta gudanar a yankin Bahar Rum.

Mr. Stoltenberg ya kuma kara da cewa, dukkan mambobin kungiyar NATO sun tsai da kudurin shiga kawancen kasashe masu yaki da kungiyar IS, NATO za ta kara marawa mambobinta baya a fannin yaki da ta'addanci, baya ga kara tura yawan jiragen sama da ke gangami kan hare-haren sama, da horar da sojojin Iraki, a kokarin tinkarar masu tsattauran ra'ayi yadda ya kamata.

Haka zakila ya ce, ya kamata kungiyar NATO ta mai da kanta matsayin wata kungiyar ba da horo, sabo da horar da sojojin wasu kasashe ya fi amfani idan aka kwatanta da aikin tura sojojin NATO zuwa kasashen wajen. Haka kuma wannan zai kasance wata hanyar da ta fi dacewa wajen hana yaduwar ta'addanci, saboda yin rigakafin ta'addanci ya fi daukar matakan soja muhimmanci.

Haka kuma Mr. Stoltenberg ya kuma furta cewa, kungiyar NATO za ta kara yawan harkokin da za ta gudanar a yankin Bahar Rum, a kokarin taimakawa kungiyar EU wajen tinkakarar matsalar 'yan gudun hijira masu satar shigowa kasashen Turai. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China