Gidan Rediyon kasar Sin watau CRI shi ne ya fassara yawancin fina-finan, tare da tantance su da za a nuna a wannan mako, kuma za a nuna wani fim mai taken "tunawa da wani karamin gari" da cibiyar Rasha da gabashin Turai ta CRI ta shirya da kuma hada da shi.
Kaza lika, shugban Gidan Rediyon CRI Wang Gengnian ya bayyana a yayin da ya halarci bikin bude makon nune-nunen fina-finan na Sin cewa, musayar fina-finai da al'adu a tsakanin Sin da Serbia mataki ne mai kyau, kuma yana fatan hakan zai zurfafa zumuncin dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu, a yayin da shugaban kasar Sin Xi Jiping yake ziyarar aiki a kasar Serbia. (Maryam)