Haka kuma, an yi gasar domin duba kwarewar daliban ajin wajen yin hira da Sinanci cikin zaman rayuwar yau da kullum, cibiyar ta kuma samar musu takardun shaidar kammala karatu bayan wannan gasa.
Mashawarcin jakadan kasar Sin kan harkokin al'adu dake Nijeriya, kana shugaban cibiyar al'adun kasar Sin na Nijeriya Yan Xiangdong, ya taya dukkan dalibai murnar kammala karatun, sannan ya kara azama kansu da su ci gaba da koyon Sinanci a nan gaba. Kaza lika, ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da yada al'adunta da Sinanci a Nijeriya, ana fatan za a sami karin 'yan Nijeriya dake koyon Sinanci a nan gaba.
Bugu da kari, ya ce, cibiyar al'adun Sin za ta zabi daliban da suka fi kwarewa don kai ziyara a kasar Sin, wadanda za su gane al'adun Sin da idanunsu.
Haka zalika, bisa labarin da aka samu, an ce, a kan bude ajin koyon Sinanci a cibiyar al'adun kasar Sin ta Nijeriya sau uku ko hudu cikin ko wace shekara, zangon karatu na ko wane aji ya kai kimanin watanni uku, kana, ya zuwa yanzu, gaba daya an yi aji sau goma, inda aka karba dalibai sama da dari uku. (Maryam)