in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhun MDD ya kalubalanci bangarorin dake gaba da juna a Yemen da su hanzarta tsagaita bude wuta
2016-09-09 13:43:52 cri
A jiya Alhamis ne, kwamitin sulhun MDD ya ba da wata sanarwa, inda ya kalubalanci bangarorin da ke gaba da juna a kasar Yemen da su tsagaita bude wuta tsakaninsu nan take, tare kuma da farfado da yin shawarwari da manzon musamman na MDD.

Sanarwar ta jaddada cewa, kamata ya yi duk wani irin matakin siyasa da za a dauka ya fito bayan yin shawarwari bisa kokarin MDD na shiga tsakani, a maimakon wani bangare ya dauki wannan mataki kawai. Kwamitin sulhu ya kalubalanci bangarorin da abin ya shafa da su sake yin alkawarin martaba yarjejeniyar daina nuna fargaba ga juna, su daina duk wani tashin hankali a wurare daban daban na kasar.

Sanarwar ta ce, kwamitin sulhu ya kara mai da hankali kan tsanantar hare-haren ta'addanci da kungiyar Al-Qaeda da IS da sauransu suka kaiwa, ya kalubalanci bangarorin Yemen da su kara mai da hankali kan aikin tsaro, domin toshe duk wata kafar kai hare-hare da 'yan ta'adda ke amfani da su. Kwamitin sulhu ya jaddada cewa, hanyar siyasace kadai za ta taimaka wajen kawar barazanar ta'addanci da Yemen ta dade tana fuskanta.

Dadin dadawa, sanarwar ta kara da cewa, muddin ba a cimma matsaya kan yadda za a aiwatar da yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya cikin dogon lokaci ba, matsalar jin kai za ta kara tsananta a sakamakon rikicin da ke faruwa a Yemen. Kwamitin sulhu ya yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su martaba dokokin kasa da kasa, su dauki matakai nan take domin kyautata yanayin jin kai, kuma su bullo da hanyoyin ceto masu cike da tsaro, domin taimakawa a shigar da kuma rarrabawa kayan abinci da man fetur da magunguna ga masu bukata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China