Duk da haka, a gun taron manema labaru da aka shirya, Ismail Ould Cheikh Ahmed ya sanar da cewa, za a farfado da shawarwarin tsakanin gwamnatin Yemen da kungiyar Houthis nan da wata guda.
Gwamnatin Yemen ta shelanta amincewa da daddale daftarin yarjejeniyar da MDD ta bayar ga bangarorin biyu a ranar 31 ga watan Yuli, da fatan hakan zai sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar. Amma kungiyar Houthis ta ki amincewa da wannan daftarin yajejeniyar, kuma ta bukaci a kafa hadaddiyar gwamnatin hadin kan kasar ta yadda za ta samu wakilci cikinta.
A ranar 28 ga watan Yuli, kungiyar Houthis da tsohon shugaban kasar Ali Saleh suka sanar da kafa kwamitin shugaban kasa domin kulawa da harkokin kasar. Kana a jiya ne aka nada membobin kwamitin, tare da shelanta cewa, za a kafa gwamnatin kasar a nan gaba.(Fatima)