in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na maraba da farfadowar shawarwarin neman sulhu a Yemen
2016-04-26 10:02:34 cri

Jiya Litinin 25 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya fidda wata sanarwa, inda ya nuna maraba da tsagaita bude wuta a tsakanin bangarorin daban daban na kasar Yemen, yayin da kuma farfadowar shawarwarin neman sulhu a kasar. Haka kuma, kwamitin ya sa kaimi ga bangarorin da abin ya shafa da su halarci taron shawarwarin neman sulhu cikin fahimtar juna da adalci.

Kaza lika, kwamitin ya yi kira ga bangarorin da su tsara wani shiri kan yadda za a aiwatar da ayyukan daukar matakan kiyaye tsaro, janye sojoji, mika makamai, sake ginawar hukumomin kasar da kuma yin shawarwarin siyasa da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China