A jiya, sojojin Yemen da dakarun Houthis, kowanensu sun saki fursunonin yaki 15 a lardin Al Jawf dake arewa maso gabashin kasar. Hukumomin yada labarai na bangarorin biyu sun ba da sanarwa domin tabbatar da wannan batu.
A ranar Asabar 18 ga wata, bangarorin biyu sun canza fursunonin yaki 194 a lardin Taiz, ciki har da fursunonin yaki daga kungiyar Houthis 118 da fursunonin yaki daga sojojin Yemen 76.
Musayar fursunonin yakin ya zama wani bangare na yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta Yemen dake karkashin jagorancin MDD. Bangarorin sun rabbata hannu kan yarjejeniyar a watan Afrilun bana, da fatan za a kawo karshen wannan yaki. Amma wannan yarjejeniya ba ta fara aiki ba tun daga daddale ta. Bisa shiga tsakani na MDD, yanzu ana yin shawarwari cikin lumana kan batun Yemen a Kuwait.
A watan Satumba na shekarar 2014, kungiyar Houthis ta mamaye birnin Sanaa, hedkwatar kasar Yemen. Shugaban kasar Abdu-Rabbu Mansour Hadi da 'yan majalisar dokokinsa sun yi gudun hijira zuwa Saudiya. A watan Maris na bara, Saudiya da wasu sauran kasashen duniya sun fara daukar matakan soja kan kungiyar Houthis.(Fatima)