Wata sanarwar da ma'aikatar yada labaru ta kasar Kuwait ta fitar, ta ruwaito Ismail Ould Cheikh Ahmed na cewa, bangarorin da abun ya shafa sun tattauna batutuwan siyasa, da tsaro, da fursunoni da dai sauransu.
A jiyan ne dai sojojin hadaka dake karkashin shugabancin Saudiyya suka fidda wata sanarwa, wadda ke nuna cewa da sanyin safiyar wannan rana, dakarun 'yan Huthi sun harba wani makamin roka daga Yemen zuwa wani sashi na kasar Saudiyya, sai dai dakarun tsaron samaniyyar kasar ta Saudiyya sun kange makamin. Kaza lika sun tarwatsa na'urar harbar roka ta dakarun 'yan Huthi ke amfani da ita.
Game da tsokana da dakarun 'yan Huthi ke yi ta hanyar harba makaman roka ga Saudiyya, sojojin hadakar kawancen sun ce za su kai zuciyar nesa, don ganin an ci gaba da cimma nasarar shawarwarin.
Sanarwar ta ce, dalilin da ya sa dakarun na Huthi suka harba makamin na roka yayin da bangarorin daban daban ke gudanar da shawarwari, shi ne domin su tsananta yanayin da ake ciki a yankin. (Bako)