Kakakin rundunar sojojin hadin gwiwar karkashin jagorancin kasar Saudi Arabia ya ce, kungiyar Houthi tana amfani da wannan sansani ne wajen dauka da kuma horas da yara 'yan kasar Yemen. Kaza lika, an kashe wani jagoran kungiyar a lokacin kai wannan hari.
Kafin wannan kuma, kungiyar likitoci ta nagari na kowa ta fitar da wata sanarwa a shiafinta na Twitter cewa, rundunar sojojin kawancen ta kai hari ta sama kan wata makaranta dake lardin Saada na kasar Yemen, lamarin da ya haddasa rasuwar dalibai guda 10, yayin da wasu 28 da suka jikkata, shekarunsu 8 ne zuwa 15 da haihuwa.
Daga bisani kuma, Asusun tallafawa kananan yara na MDD ya tabbatar kai harin ta sama, inda ya yi kira ga bangarorin da rikicin kasar Yemen ya shafa da su martaba dokokin kasa da kasa, kana su daina illa ga fararen hulan kasar.
Bugu da kari, rahotanni na cewa, a ranar 13 ga wata, rundunar sojojin hadin gwiwar dake karkashin jagorancin kasar Saudi Arabia ta kai hare-hare ta sama har sama da sau 100 a wurare daban daban dake arewacin kasar Yemen, ciki har da babban birnin kasar, Sanaa. (Maryam)