A yau Asabar shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma wanda ya zo nan kasar Sin domin halartar taron koli na G20 da za a fara a birnin Hangzhou.
Xi Jinping ya bayyana cewa, kasarsa na dora muhimmanci sosai kan huldar dake tsakanin kasashen biyu, tana kokarin raya huldar don ta zama irin ta abokantaka da kuma 'yan uwantaka.
Shugaba Xi ya kuma jaddada cewa, kasar Sin da kasashen Afrika sun nace ga yin hadin gwiwa da neman samun moriya tare, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan aikin neman samun bunkasuwa da shimfida zaman lafiya a kasashen Afrika. Kasar Sin da kasar Afrika ta kudu dukkansu kasashe membobi ne na kungiyar BRICS. Kasar Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasar Afrika ta kudu kan harkoki na tsakanin kasa da kasa, domin raya huldarsu zuwa gaba, da ingiza hadin gwiwar kasashen kungiyar BRICS, da kuma cimma burin kara samun sakamako mai kyau ta hanyar yin hadin gwiwa a cikin kungiyar G20.
A nasa bangare, shugaban Afrika ta kudu Jacob Zuma ya bayyana cewa, kasar Afrika ta kudu tana dora muhimmanci sosai a kan huldar abokantaka a tsakaninsu., kana tana jinjina wa kasar Sin wajen ba da gudummawa ga kasashen Afrika, da kuma mayar da batutuwan neman samun bunkasuwa tare da tabbatar da shirin neman samun bunkasuwa mai dorewa na MDD kafin shekarar 2030 a matsayin muhimman batutuwan da za a tattauna a gun taron G20. Kasar Afrika ta kudu tana son yin hadin gwiwa tare da Sin a karkashin laimar MDD da kungiyar G20 da kungiyar BRICS da dandalin tattaunawar hadin gwiwar tattalin arzikin Sin da Afrika da kuma sauran kungiyoyin kasa da kasa.(Lami)