Game da taron koli na kungiyar G20 da ake daf da budewa a birnin Hangzhou, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Sin madam Hua Chunying, ta bayyana a yau Jumma'a 2 ga wata cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai gana da takwaransa na Amurka Barack Obama a birnin na Hangzhou. Ta ce yanzu haka hukumomin kasashen biyu na ci gaba da tuntubar juna game da wannan batu.(Fatima)