Shugabar sashi mai kula da dangantaka tsakanin Sin da Afrika a kudancin Afrika Madam Phyllis Johnson, ta ce taron G20 da za a kira, zai zama wani mataki da Sin ta dauka, da zummar amfani da karfinta don neman moriya ga kasashe masu tasowa, ciki hadda kasashen nahiyar Afrika,
Phyllis ta ce, Sin tana kokarin sa kaimi ga mu'ammala tsakanin ta da kasashe masu wadata, da ma kasashe masu tasowa, kuma taron kolin na wannan karo zai daga dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika zuwa wani sabon matsayi.
Yayin da ake kusantar taron G20, Madam Phyllis Johnson, ta shaidawa manema labaru na gidan rediyon kasar Sin cewa, ganin Afrika ta kudu ce kadai kasa daya tilo mamba a kungiyar daga nahiyar Afrika, ya sa Sin ta gayyaci wasu shugabannin kasashen Afrika da dama da su halarci taron.
Har wa yau, a cewar ta, Sin ta kasance kasa dake da karfi matuka a fannoni daban-daban, wanda hakan ya sa take da matsayi mai girma a duniya, wanda ba za a iya maye gurbinta ba, don haka kasar ta Sin ta kai ga kulla dangantaka cikin adalci tsakanin ta da kasashe daban-daban, tare da kafa wani dandalin gudanar da mu'ammala tsakanin kasashen daban-daban. (Amina)