Yayin zantawar ta su, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, kasashen Sin da Senegal, sun samu ci gaba matuka a fannin gudanar da hadin gwiwa a dukkan fannoni. Kaza lika kasar Sin tana fatan raya huldar dake tsakanin ta da Senegal, zuwa huldar abokantaka ta hadin gwiwa a dukkan fannoni, da tabbatar da nasarar sakamakon da aka samu a gun taron koli na dandalin tattaunawa na hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika na Johannesburg, da ma zurfafa hadin gwiwar da ka iya haifar da moriyar juna a tsakaninsu ta yadda al'ummun su za su amfana.
A nasa tsokaci shugaba Macky Sall ya bayyana farin cikinsa, bisa gayyatar da shugaba Xi ya yi masa zuwa taron kolin na G20, ya ce hakan ya shaida cewa, Sin na dora muhimmanci sosai game da kasashen Afrika. Shugaba Sall ya kara da cewa Senegal na jinjinawa Sin, bisa goyon baya da take nuna mata. Ta kuma yaba da shirin hadin gwiwa da kasar Sin ta gabatar a gun taron koli, na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afrika na Johannesburg da ya gudana a bara. Har ila yau kasar sa na fatan ci gaba da hadin gwiwa tare da Sin a fannonin samun bunkasuwarta.(Lami)