Jaridar Huffington Post ta Amurka ta gabatar da wani bayani mai taken "Taron kolin G20 a birnin Hangzhou zai karfafa dangantakar abokantaka a yanayin tangal tangal", inda aka bayyana cewa, a yanayin tangal tangal da ake ciki yanzu haka a duniya, gudanar da taron kolin G20 a birnin Hangzhou zai samar da wani muhimmin zarafi na kafa dangantaka ta hakuri da daukar alhaki tsakanin manyan kasashen duniya, kuma zai samar da yanayi mai kyau wajen kulawa da harkokin duniya ta hanyoyin zamani. Bayanin ya ce, gudanar da wannan taron koli a kasar Sin ya dace sosai, sabo da karuwar tattalin arzikin Sin za ta kara kwarin gwiwar kasa da kasa.
A yayin da yake zantawa da wakilin gidan telabijin na kasar Afirka ta kudu, mataimakin ministan harkokin waje na kasar, Luwellyn Landers ya bayyana cewa, Afirka ta Kudu na fatan wannan taron koli zai tabbatar da karuwar tattalin arzikin duniya, musamman ma ga kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa, tare da daidaita matsalar rashin karfin bunkasuwar tattalin arziki na wasu kasashen duniya.(Fatima)