in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta kudu za ta jawo hankalin shugabannin G20
2016-09-02 15:00:27 cri

Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma, ya ba da wata sanarwa a jiya Alhamis 1 ga watan nan, wadda ke cewa, Afrika ta kudu za ta yi kokarin jawo hankalin shugabannin G20, a taron koli da za a yi a birnin Hanzhou, yana mai fatan taron zai fitar da wani shiri na raya tattalin arzikin kasashen Afrika, da kuma dukkanin kasashe masu tasowa.

Bisa labarin da aka bayar, an ce yayin taron, shugaba Zuma zai gana da sauran shugabannin BRICS. Kuma ya yi shirin tattauna da kasar Chadi wadda ke rike da shugabancin AU, da kuma kasar Senegal, wadda ke rike da shugabancin kungiyar tsara shirin raya Afrika. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China