Babban sakataren kungiyar hadin gwiwa da neman bunkasuwar tattalin arzikin duniya Jose Angel Gurrra Trevino ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, a matsayinta na kasar dake shugabantar kungiyar G20 a wannan karo, kasar Sin ta taka rawar a zo a gani.
Ya kuma kara da cewa, a cikin halin tabarbarewar tattalin arzikin duniya, dora muhimmanci a kan batun farfado da tattalin arziki a gun taron koli na G20 na birnin Hangzhou na da muhimmanci sosai. Ya ce, za a yi wannan taro ne a daidai lokacin da ake lallubo bakin zaren daidaita batutuwan tattalin arziki da ciniki a fannoni da dama, ana sa ran kasashe membobin G20 za su tsara shirin da zai iya raya tattalin arzikin duniya cikin dorewa tare da kiyaye muhalli.
Jose Angel Gurrra Trevino ya kara da cewa, kasar Sin tare da kasashe membobin G20 suna tuntubar kungiyoyin duniya da suka hada da kungiyar hadin gwiwa da neman bunkasuwar tattalin arzikin duniya, domin neman wata hanyar neman bunkasuwar tattalin arziki da ciniki cikin sauri, wannan shi ne wani muhimmin sakamakon da Sin ta samu a matsayin kasar dake rike da shugabancin kungiyar G20.(Lami)