in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron kolin G20 zai ba da taimako wajen tabbatar da dauwamammen ci gaban duniya
2016-09-01 16:16:04 cri
Za a gudanar da taron kolin G20 a birnin Hangzhou na kasar Sin tun daga ranar 4 zuwa ta 5 ga watan Satumba, mataimakin babban magatakardan MDD mai kula da harkokin tattalin arziki da zaman takewar al'umma Wu Hongbo ya bayyana cewa, taron kolin G20 da za a yi zai ba da taimako matuka ga kasa da kasa wajen cimma burin neman dauwamammen ci gaba.

Haka kuma, ya ce, a matsayin kasa mai shugabancin kungiyar G20 na wannan karo, kasar Sin tana mai da hankali matuka kan batun neman dauwamammen ci gaban duniya, shi ya sa, taron da za a yi zai ba da gudunmawa kai tsaye ga kasa da kasa wajen aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba na shekarar 2030 bisa fannoni daban daban, da kuma yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China