Wannan ne karo na farko da kasar Sin za ta karbi bakuncin gudanar da taron kolin na G20, kana shi ne batun diplomasiyya mafi muhimmanci ga kasar ta Sin a bana. Hakan ne kuma ya sa aka dauki matakan tabbatar da tsaro a matsayin koli, a yayin taron kolin na G20.
Ga misali, za a yi amfani da fasahar gano asalin mutane ta hanyar duba fuska, domin kara tabbatar da tsaro a muhimman yankuna. Kana hukumomin da abun ya shafa, za su inganta tsarin rajistar sunaye na gaskiya, wanda za a yi amfani da shi a Otel Otel, da a wuraren sufuri, da hidimar samar da yanar gizo da dai sauransu.
Kaza lika domin kandagarkin faruwar al'amura na ba tsammani, an kafa wani rukuni na sintiri a birnin Hangzhou, inda tuni 'yan sandan birnin suka yi gwajin aikin tashoshin bincike a hanyoyin motoci guda 172, don tabbatar da tsaro a dukkan hanyoyin motoci dake birnin. (Zainab)