in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan bangarori daban daban za su taka rawa da ta dace a taron G20
2016-08-30 20:43:53 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a gun taron manema labaru da aka yi a yau Talata cewa, kasar Sin na fatan bangarori daban daban, za su sauke nauyin dake wuyansu, domin tabbatar da nasarar taron kungiyar G20 cikin nasara.

Hua Chunying ta bayyana hakan ne yayin da wani 'dan jarida ke tambaya game da tsokacin kamfanin dillancin labarai na Reuters, wanda a jiya Litinin ya ce ko da yake kasar Sin na son nuna matsayinta na babbar kasa a duniya ta hanyar gudanar da taron G20 cikin nasara, a hannu guda Sin din na damuwa game da wasu kalubale da kasashen yamma za su kawo mata. Ya ce ko mene ne ra'ayin Sin a game da hakan?

Game da hakan, Madam Hua ta bayyana cewa, kasashen Amurka da Ingila da Canada da Japan, da ma sauran kasashe membobin kungiyar G20 sun sha yin hadin gwiwa, da musayar ra'ayi tare da Sin, game da shirin gudanar da taron G20, kana sun sanar da cewa, za su goyi bayan Sin wajen ganin an cimma nasarar taron yadda ya kamata.

Ta ce a kwanakin baya, babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon, ya jinjinawa karfin jagoranci da Sin ta nuna, a yayin da take shirya taron na G20. Ya ce bisa gudunmawar da Sin ta bayar, baya ga tattaunawa kan yadda za a tinkari matsalar hada-hadar kudi, hakan zai kuma bada damar yin hange nesa, kan bunkasuwar tattalin arzikin duniya a nan gaba, da ma a tsawon lokaci mai zuwa. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China