in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a samar da fasahohi da zarafi ga kasashe masu tasowa a gun taron kolin G20
2016-08-30 15:31:55 cri
A bisa halin rashin bunkasuwar tattalin arzikin duniya, farfesa Khairy Tourk, masani kan harkokin tattalin arziki a kwalejin injiniya dake Illinois na kasar Amurka ya bayyana a kwanakin baya cewa, za a bullo da sabbin hanyoyin da za su taimaka ga samun ci gaba a duniya a gun taron kolin kungiyar G20 da za a gudanar a birnin Hangzhou na kasar Sin.

Tourk ya bayyana cewa, yana farin ciki sosai da yadda aka shigar da batun raya masana'antu na kasashe maso tasowa a matsayin manyan batutuwan da za a tattauna a gun taron kolin G20 da za a gudanar a birnin Hangzhou, a ganinsa, samun ci gaba da yadda kasar Sin ke yiwa tsarin tattalin arzikinta kwaskwarima za su samar da fasahohi da dama ga sauran kasashe masu tasowa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China