Mataimakin mai ba da shawara kan harkokin tsaro game da dabarun sadarwa Ben Rhodes ya shaidawa taron manema labarai cewa,shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na Amurka Barack Obama za su yi wata ganawa mai zurfi a jejiberen taron kolin G20 da za a bude a mako mai zuwa a birnin Hangzhou da ke nan kasar Sin. Daga bisani kuma, ana saran shugaba Obama zai halarci wata 'yar karamar liyafar cin abincin dare da mai masaukinsa shugaba Xi ya shirya masa.
Jami'in ya ce, a yayin wannan ganawa za a gina kan abubuwan da shugabannin biyu suka tattaunawa a yayin da Obaman ya ziyarci Beijing,ciki har da sanarwar hadin gwiwa kan canjin yanayi da abubuwan da shugabannin biyu suka a yayin ziyarar shugaba Xi a kasar ta Amurka.
Ana kuma saran a lokacin taron kolin na G20,shugabannin biyu za su yi bitar dukkan batutuwan da suka shafi hadin gwiwar kasashen biyu cikin shekaru 7 da rabi da suka gabata.
Bugu da kari, shugabannin biyu za su nazarci irin ci gaban da aka samu a tattalin arzikin duniya, canjin yanayi, kokarin hana yaduwar makaman nukiliya ta hanyar yarjejeniyar da aka cimma da kasar Iran, da kuma damuwar da ake da shi kan halin da ake ciki a zirin Koriya.(Ibrahim)