Chen Fengying, wata manazarciyar huldar kasa da kasa tana ganin cewa, kasar Sin a yanzu haka tana mai da hankali kan kirkiro sabbin fasahohi don samun ci gaban tattalin arziki. Hakan a cewarta na nufin yadda za a yi amfani da wasu damammakin da suka shafi cigaban wasu fasahohin masana'antu, da tattalin arzikin da ake kokarin raya shi bisa tushen alkaluma, don kirkiro sabbin fasahohi, ta yadda za a samar da wani sabon tsarin da zai sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.
A nasa bangare, Zhao Xijun, masani a fannin hada-hadar kudi na jami'ar jama'a ta kasar Sin ya ce, yanzu kasar Sin ta dora muhimmanci sosai ga manufar gyara tsarin tattalin arziki a kasar, wadda ta kasance daya daga cikin muhimman manufofin kasar, ban da manufofin kudi da na harkar hada-hadar kudi. Don haka yana sa ran ganin kasar Sin ta gabatar da shawarar gyara tsarin tattalin arziki a wajen taron na G20 don neman kyautata yanayin tattalin arzikin duniya.(Bello Wang)