Brennan ya gaya wa kwamitin kula da aikin leken asiri na majalisar dattawa ta kasar Amurka, cewar kungiyar IS tana da dimbin mabiya masu dauke da makamai wadanda za su iya daukar matakan kai hare-hare a kasashen yammacin duniya. Ya yi gargadin cewa, mai yiyuwa membobin kungiyar IS za su shiga kasashen yammacin duniya a matsayin 'yan gudun hijira.
Bisa alkaluman da Mr. Brennan ya bayar, an ce, ko da yake kungiyar IS, ta rasa yankuna da yawa a kasashen Sham da Iraki, amma har yanzu tana da dakaru masu dauke da makamai wajen dubu 18 zuwa dubu 22, kuma reshenta dake kasar Libya na da dimbin makaman zamani masu hadari sosai.
Direktan hukumar CIA ya kimanta cewa, akwai masu dauke da makamai na kungiyar IS wajen dubu 5 zuwa dubu 8 dake zaune a kasar Libya wadda take kusa da kasashen Turai sosai. Sannan akwai wasu dubu 7 da suke kasar Najeriya, da daruruwa suna kasar Masar da Afghanistan da Pakistan. (Sanusi Chen)