Kungiyar hada kan kasashen Larabawa AL da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ne suka shirya wannan dandali na kwanaki biyu.
A jawabinsa yayin taron mataimakin shugaban kasar Sudan Mista Bakri Hassan Salih ya bayyana cewa, a koda yaushe kasar Sudan tana ba da muhimmanci sosai kan aikin dakile ta'addanci, kana irin matakan da take dauka a 'yan shekaru nan sun taimaka wajen hana yaduwar ayyukan ta'addanci, musamman ma a arewacin yankin Darfur dake dab da kasar Libya.
A nasa jawabin, mataimakin babban sakataren AL Mista Ahmed Ben Helli, ya yi kira ga kasashe mambobin AL da su kara hada kai don yaki da ta'addanci. Ya ce, ya kamata kasashe mambobin kungiyar su hada kai tare da bullo da manufofin da suka dace don hana yaduwar ayyukan ta'addanci, ciki hadda matakan siyasa, aikin soja, tattalin arziki, yada labarai da dai sauransu. (Amina)