in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD na bincike game da harin da aka kaiwa tawagar wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu
2016-08-18 20:00:19 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki Moon, ya sanar da bude wani bincike na musamman, game da harin da aka kaiwa tawagar wanzar da zaman lafiya ta UNMISS, a wani otal dake Sudan ta kudu. Ban Ki moon ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fitar a birnin Juba.

A ranar 11 ga watan Yulin da ya gabata ne dai aka kaiwa jami'an tawagar ta UNMISS hari a otel, wanda hakan ya sabbaba rasuwar mutum guda, kana maharan suka ci zarafin wasu fararen hula, ta hanyar fyade, da lakadawa wasu dukan kawo wuka.

Bayan aukuwar harin ne kuma aka fara samun zarge zarge dake nuna sakaci da aiki a bangaren dakarun na UNMISS, wanda hakan ne kuma ya sanya Mr. Ban kaddamar da binciken musamman, da nufin gano hakikanin al'amarin, da ma auna sahihancin daukacin ayyukan da tawagar ta wanzar da zaman lafiya a Sudan ta kudu ke gudanarwa a kasar.

A daya bangaren kuma, Mr. Ban ya yi kira ga mahukuntan Sudan ta Kudu, da su gudanar da bincike na hakika, game da duk wasu zarge zarge dake da nasaba da cin zarafin al'ummar kasar, su kuma hukunta dukkanin masu hannu cikin aikata hakan.

Ba dai wani mutum guda da aka taba hukuntawa, tun bayan barkewar yakin basasar da ya barke a Sudan ta Kudu.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China